Philippians 4

1Saboda haka ʼyanʼuwana, ku da nake ƙauna, nake kuma marmarin ganinku, ku da kuke farin cikina da kuma rawanina, ku dage ga Ubangiji, ya ku ƙaunatattuna!

Gargaɗi

2Ina roƙon Yuwodiya ina kuma roƙon Sintike, su yi zaman lafiya da juna saboda su na Ubangiji ne. 3I, ina kuma roƙonka, abokin famata, ka taimaki matan nan waɗanda suka yi fama aikin bishara tare da ni, haka ma Kilemen da kuma sauran abokan aikina, waɗanda sunayensu suna cikin littafin rai.

4Ku yi farin ciki a cikin Ubangiji kullum. Har wa yau ina dai ƙara gaya muku, ku yi farin ciki! 5Bari kowa yǎ kasance da sauƙinkai. Ubangiji ya yi kusan zuwa. 6Kada ku damu game da kome sai dai a cikin abu duka, ku gabatar da roƙe roƙenku ga Allah ta wurin adduʼa da roƙo, tare da godiya. 7Salamar Allah, wadda ta wuce dukan fahimta, za ta tsai da zukatanku da tunaninku cikin Kiristi Yesu.

8A ƙarshe, ʼyanʼuwa, duk abin da yake na gaskiya, duk abin da yake na girmamawa, duk abin da yake daidai, duk abin da yake da tsarki, duk abin da yake kyakkyawa, duk abin da yake na shaʼawa-in ma wani abu mafifici ne, ko ya cancanci yabo-ku yi tunani a kan irin abubuwan nan. 9Duk abin da kuka koya ko kuka karɓa ko kuka ji daga wurina, ko kuka gani a cikina-ku yi aiki da shi. Allah na salama kuma zai kasance tare da ku.

Godiya saboda Kyautayinsu

10Na yi farin ciki sosai ga Ubangiji don yanzu kun sāke nuna kun kula da ni. Ko da yake dā ma kun kula da ni sai dai ba ku sami dama ku nuna mini ba. 11Ba na faɗin haka domin ina cikin bukata, gama na koya yadda zan gamsu a cikin kowane hali. 12Na san mene ne zaman rashi, na kuma san mene ne zaman samu. Zan iya zama cikin kowane hali, ko cikin ƙoshi ko cikin yunwa, ko cikin yalwa ko kuma cikin fatara. 13Ina iya yin kome ta wurin wannan wanda yake ba ni ƙarfi.

14Duk da haka kun kyauta da kuka yi tarayya da ni cikin wahalolina. 15Ban da haka, kamar yadda ku Filibbiyawa kuka sani, a farkon kwanakin da kuka ji bishara, saʼad da na tashi daga Makidoniya, babu wata ikkilisiyar da ta yi tarayya da ni a fannin bayarwa da karɓa, sai ku kaɗai; 16gama ko saʼad da nake a Tassalonika ma, kun aiko mini da taimako sau da sau saʼad da nake cikin bukata. 17Ba cewa ina neman kyauta ba ne, sai dai ina neman abin da za a ƙara a kan ribarku. 18An biya ni duka, biyan da ya wuce misali. Bukatata ta biya, da yake na karɓi kyautarku da kuka aiko ta hannun Afaforiditus. Baiwa mai ƙanshi, hadaya abar karɓa, mai faranta wa Allah rai. 19Allahna kuma zai biya dukan bukatunku bisa ga ɗaukakar wadatarsa cikin Kiristi Yesu.

20Ɗaukaka ta tabbata ga Allahnmu da Ubanmu har abada abadin. Amin.

Gaisuwa Ta Ƙarshe

21Ku gai da dukan tsarkaka cikin Kiristi Yesu. ʼYanʼuwan da suke tare da ni suna gaishe ku. 22Dukan tsarkaka suna gaishe ku, musamman waɗanda suke na gidan Kaisar.

23Alherin Ubangiji Yesu Kiristi yǎ kasance da ruhunku. Amin.
Waɗansu rubuce rubucen hannu na dā ba su da Amin.


Copyright information for HauSRK